Hukumar kidayar jama’a, ta Najeriya, tace an samu raguwar mutuwar mata wajen haihuwa, a jihar Nejar.
WASHINGTON, DC —
Hukumar kidayar jama’a, ta Najeriya, tace an samu raguwar mutuwar mata wajen haihuwa, a jihar Neja.
A lokacin mika rahoton wani bincike da hukumar kidayar jama’a, tayi akan batun mace-macen mata, a wurin haihuwa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, hukumar tayi na'am da sakamakon binciken.
Hukimar kidayar ta ce duk da yake har yanzu akwai sauran aiki, amma mutuwar matan a wurin haihuwa, ya ragu da kashi 63 a cikin 100, a jihar ta Neja.
Shugaban hukumar kidayar jama’a, na Najeriya, mai kula da jihar ta Neja, Barrister Umaru Datti, yace an samu gagarumin nasara idan aka kwatanta da shekarun baya.
Your browser doesn’t support HTML5