Shugaban sashen gudanarwa da ayyukan tsaro na MDD a Najeriya, Mathew Alao, ya bayyana hakan yayin yaye wasu ‘yan kato da gora da aka fi sani da civilian JTF su 123 daga jihar Borno, a cibiyar koyar da dabarun shugabanci da zama ‘dan kasa na gari, dake Shere Hills a jihar Pilato.
Jami’in MDD ya ce a baya, ‘yan kato da goran na aiwatar da hukunci ne ba tare da la’akari da doka ba, amma tun da suka fara samun wannan horo, sukan mika wa hukumomi duk wanda suka kama don gudanar da bincike da aiwatar da hukunci.
‘Yan kato da goran sun sami horo ne kan sasanta al’umma da inganta zamanta kewa da sana’oi da kuma dabarun dakile tashe-tashen hankali a Arewa maso Gabas.
Domin Karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5