Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce adadin wadanda suka kamu da COVID-19 a kasar ya kai 18,480.
Adadin ya kai wanann matakin ne bayan da aka samu karin mutum 745 da suka kamu da cutar a jihohi 21, ciki har da Abuja babban birnin kasar.
Jihohin da aka gano sabbin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Legas inda aka samu mutum 280, 103 a Oyo, 72 a Ebonyi, 60 a Abuja, 46 a Imo, 34 a Edo, 33 a Delta, 25 a Rivers, 23 a Kaduna, 16 a Ondo, 12 a Katsina, 10 a Kano.
Sauran jihohin sun hada da Bauchi mai mutum 8, 7 a Borno, 5 a Kwara, 4 a Gombe, 2 a Sokoto da Enugu, da kuma 1 a Osun, Nasarawa da Yobe.
Wannan dai shine adadi mafi yawa da aka samu a rana daya tun bayan da wasu jihohin kasar suka fara sassauta matakan kulle saboda dakile yaduwar cutar annobar ta COVID-19.
Sanarwar da hukumar ta fidda a shafinta na Twitter ranar Alhamis 18 ga watan Yuni ta kuma ce ya zuwa yanzu an sallami mutum 6,307 daga asibiti kana mutum 475 sun mutu.