Kauyuka 4 ne lamarin ya shafa, da suka hada da Rakonni, Tsagi, da Kalhu da kuma Gi’ire, duk a cikin gundumar Gandi da ke karamar hukumar mulki Tarabah, inda ‘yan bindigar da ba’a gane adadinsu ba.
Masu bindigogin dai, sun fara kashe mutane 18 ne ranar Asabar da ta wuce, sai kuma jiya lokacin da a ke jana'izarsu, suka dawo suka sake bude wuta a kan jama'a, inda mutum 4 suka rasa ra'ikunsu.
Wakilin Muryar Amurka ya ce kananan hukumomin da ke Zamfara, sun dade suna cikin wannan al'amarin kai hari daga 'yan bindigan, kuma sun dauka abin ya lafa, amma sai kuma suka sake samun hari wanda har ya shafi sauran hukumomin da ke kusa da su.
Yanzu haka ana zaman dardar a garuruwa da dama a yankin gabashin jihar Sokoto saboda fargabar kai hari a kowane lokaci, yayin da wasu al’ummomi da dama suka bar garuruwansu.
Ga cikkaken rohoton wakilin Muryar Amurka Murtala Faruq Sayinna
Your browser doesn’t support HTML5