Kasar kamaru tana da kimanin mutane miliyan ishirin da biya, ban da kimanin ‘yan gudun hijiya dubu dari uku da hamsin da suka kauracewa kasarsu Afrika da tsakiya, da kuma kimanin ‘yan gudun hijira dubu dari da suka gujewa hare haren Boko Haram a Najeriya. Har wa yau, akwai ‘yan gudun hijira na cikin gida dubu dari uku da kungiyar Boko Haram da kuma tashe tashen hankali da ‘yan aware daga yankin dake amfani da harshen ingilishi na kasar suka haddasa.
Sama da likitoci dari biyar da kuma ma’aikatan jinya-nus-nus dubu biyar ake horaswa a kasar Kamaru kowacce shekara. Sai dai a shekarar alib da dari tara da casa’in da shida, da kasar ta fuskanci komadar tattalin, aka zaftare albashin likitoci da kashi sittin cikin dari, zuwa kimanin dala dari uku a wata, sabili da haka, da dama suka kaura zuwa kasashen waje, har yanzu wadansu suna tafiya wadansu kasashe sabili da karancin albashi.
A watan Agusta, hukumomin kasar suka fitar da rahoto cewa, ma’aikatan jinya suna kauracewa asibitai a yankunan da ake amfani da harshen ingilishi, biyo bayan hare haren da aka kashe ma’aikatan jinya da dama, aka kuma raunata wadansu tari.