Al'amarin ya auku ne bayan kama dan kasuwar da kuma yanke ma sa hukuncin tafiya gidan yari saboda kasa kaya barkatai.
Wani ganau ya bayyana yanda akasin ya auku, inda jami'an 'yan sanda na kwamitin aiki da cikawa su ka kama dan kasuwar da mika shi ga kotun tafi da gidan ka wacce ta yanke ma sa hukuncin tafiya gidan yari.
Lokacin da 'yan sanda su ka saka mutumin mai suna Oga Musa a mota sai ya yi tsalle ya diro daga motar don arcewa inda 'yan sanda su ka harbe shi ya mutu nan take.
Hakan ya harzuka 'yan kasuwa har su ka bankawa ofishin 'yan sanda na kasuwar wuta.
Da na tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Abuja, Josephine Adah, sai ta ce, "Kiran da ka ke yi na kawo tangarda ga binciken da na ke yi. Na ji wuta ta kama a kasuwar Wuse zan kira ka in mun gama bincike."
Shugaban kungiyar 'yan kasuwar arewa reshen Abuja Alhaji Adamu Hassan ya bayyana takaici kan kashe dan kasuwar da kuma shirin daukar matakin da ya dace.
Masu sayan kaya da 'yan kasuwar da dama sun gaggauta ficewa daga kasuwar don 'yan sanda sun shiga jefa hayaki mai sa kwalla.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5