Hukumomi a Najeriya na sun bayyana cewa an samu rahoton bullar kwayar wata nau’in cuta dangin Polio a Jihohin Najeriya 19.
Bauchi na daya daga cikin jihohin da nau'in cutar mai suna Polio Virus Type 2 ya bulla a yankunan kananan hukumomi 12 a jihar.
Kananan hukumomin da aka gano kwayar cutar Polio mai au’in Cmpv2 su ne Toro, Warji, Darazo, Misau, Dambam, Zaki, Jama’are, Alkaleri, Ganjuwa, Bauchi, Katagum, da kuma Shira.
Yayin tattaunawa da Shugaban Hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Bauchi Dr. Rilwan Mohammed ta wayar taraho, ya ce an dukufa ka’in dana na’in wajen wayar da kan jama’a tare da hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, yayin da aka kaddamar da Allurar rigakafi akan iyakokin Makwabtan jihohi.
Dr. Rilwan Muhammed ya ce ba Polio ba ce aka samu an samu alamarta ne tana nan bata tafi ba, kwayar cuta ce mai yawo, an samu guda 38 a Jahar Bauchi.
Saurari cikekken bayana cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5