‘Yan gudun hijirar dai nada ra’ayi daya, na fatan lamura su daidai ta a garuruwansu, domin su koma gida.
A sakamakon rikice rikicen kabilanci, da gaba tsakanin manoma da makiyaya, zuwa mafi muni rashin tsaro daga hare-haren ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram, ya sanya ‘yan gudun hijira a Najeriya dake cikin gida da wanda suka tsallake, ya haura dubu dari bakwai.
Tabakin kwamishinar kula da ‘yan gudun hijira ta Najeriya, Hadiza Sani Kan Giwa tace, “a kwai mata da yara da suka rasa mazajensu da iyayensu, akwai maza da suka rasa matsugunni suka rasa sana’a, wasu kuma basu da lafiya, gwamnatin tarayya tana iyakacin kokarinta, banda hukumarmu, akwai hukumomi dayawa, akwai hukuma kamar NEMA, kuma kusan kowacce hukuma ta gwamnatin tarayya, tana iyakacin kokari taga cewa anshawo kan wannan al’amari, to amma ance in danbu yayi yawa ance bayajin mai.”
Rashin tsaro a yankuna da dama na Najeriya, na matukar illa ga ilimi, harkokin kiwon lafiya da tattalin arziki.
Your browser doesn’t support HTML5