Bayanan na cewa mutane na kara kamuwa da cutar ne sakamakon matsalar zafi da ake fama da ita, a wannan lokaci koda yake hukumomin jahar na cewa lamarin bai kai matsayin annoba ba, kuma sun ce suna daukar matakin gaggawa a duk inda aka samu bayanan bullar cutar.
Da yake tabbatar da bullar cutar Dr Raymon Dauda, wani likita kuma shugaban asibitin Vanada Hospital, wanda ke zaman kansa a Yola, yace ya zuwa yanzu sun yi jinyar wasu da suka kamu da cutar.
Ko wadanne matakai ya kamata jama’a su dauka don yin rigakafin kamuwa da cutar?, masanin kiwon lafiya Dr Raymon Dauda, ya bayyana cewa mafi yawancin alkalumman gwamnati na bayyana yawan wadanda suka mutu a asibiti a yayin da wasu ke mutuwa a gidajensu saboda rashin abin hannu da za su dauki dawainiyar kansu a asibiti.
To sai dai kuma, yanzu haka hukumomin lafiya na daukar matakai na shawo kan matsalar ta hanyar riga kafi da ba da magani da kuma yekuwar wayar da kai a kan kaucewa kwanciya a cikin dakuna saboda tsananin zafi. Dr Fatima Atiku Abubakar, itace kwamishiniyar kiwon lafiya a jihar Adamawa, ta bayyana matakan da suka dauka.
Kamar yadda alkalumman cibiyar kare cututtuka ta Najeriya, ke nunawa, ya zuwa yanzu kusan fiye da Mutum 260 ne suka mutu a Najeriya, sakamakon cutar sankarau, yayin da hukumar tace kusan mutane dubu 2 ne ake kyautata zaton sun kamu da cutar ta sankarau a cikin wannan shekarar. Kuma jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina da Kebbi da kuma Neja, su ne suka fi fama da cutar a wannan karon.
Ibrahim Abdul’aziz na da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5