An Sako Matan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace a Kan Iyakar Nijar Da Najeriya

Matan nan da ‘yan bindiga suka abkawa cikin gidansu kuma suka yi garkuwa da su a kan iyakar Nijar da Najeriya sun kubuta bayan an biya kudaden fansa.

An kubutar da Matan ne bayan an biya kudi tsaba naira miliyon 2 kamar yadda daya daga cikin makusantan mutanen da a ka sace yayi bayyani.

Lamarin ya faru ne a kan iyakar Nijar da Najeriya a garin Kalmalaw ta karamar hukumar Mulkin Illela cikin jihar Sokoto Tarrayar Najeriya kilomita 3 kawai da Jamhuriyar Nijer.

Matan da a ka sace a makon jiya, bayan maharansu 7 dauke da manyan bindigogi sun share lokaci, suna barin wuta, don mutane su tsorata.

Lamarin da ke kasancewa na farko a garin Kalmalaw, ya sa garin fadawa a wannan lokacin a cikin yanayin makoki, domin jama'ar garin sun shiga zullumi mai zurfin gaske.

Har yanzu dai, ‘yan bindiga na ci gaba da cin karensu ba babbaka a wannan yankin duk da matakan aikin sa-kai da matasan garuruwa da dama suka shiga, don hana irin wannan lamarin aukuwa.

A saurari rahoto cikin sauti daga Mamane Harouna:

Your browser doesn’t support HTML5

An Sako Matan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace a Kan Iyakar Nijar Da Najeriya


Karin bayani akan: Jamhuriyar Nijer​, Nigeria, da Najeriya.