Tsohon ‘dan wasan kwallon kafar Afirka ta Kudu ya shiga tarko inda akayi masa fashi da makami a wani shagon aski dake birnin Johannesburg.
McCarthy mai shekaru 37 dai ya koma kasar sa a matsayin mai sharshi kan gasar kalubalen kwararru ta champion League ga wani gidan talabishin, ya dai sami zama zakaran wannan gasar a shekara ta 2004 locacin da yake Porto.
An dai kwace masa wasu sarkoki da wasu kayayyakin dake jikin sa a lokacin amma ba’a taba lafiyar sa ba.
Abokin McCarthy da yake tare da shi alokacin fashin yace, “’daya daga cikin ‘yan fashin ne ya tunkareshi ya kuma saka masa bindiga a kunnen sa, ya umarce shi daya bashi sarkokinsa da agogon sa, yana jin haka ya rufe hannun sa domin ya boye zoben aurensa kasancewar zoben nada tamani ko daraja gare shi, ‘dan fashin yace bani zoben sai ya ciro ya bashi.”
‘yan sanda dai na binciken wannan al’amari da ya faru, wanda yazo wata shida bayan da aka kashe mai tsaron gida na Afirka ta kudu alokacin da ake musu fashi a gidan budurwar sa dake garin Soweto.