Shedun gani da ido dai sun tabbatar da cewa harin ya tarwatsa wurare biyu a garin Aden dake gabar teku inda fadan yake ci gaba da wakana tsakanin ‘yan Houthi da sojoji masu goyon bayan hambararriyar gwamnatin Yemen.
Hare-haren na tsawo wata guda ya yi sanadiyyar mutuwar daruwan mutane da kuma haddasa matsalolin rayuwar jama’ar Yemen ba tare da cimma gaci ba wajen dakile ‘yan tawayen Houthin.
‘Yan shi’ar sun kwace ikon yawancin garuruwan Yemen tare da samun nasarar korar shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi da Yammacin duniya ke marawa baya zuwa Saudiyya.
Ana dai kyautata zaton ‘yan Houthi din na da goyon bayan Iran wanda aka ga jirgin yakinsu ya nufi tekun Yemen.
Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter ko a jiya ya bayyana damuwar Amurka a kan wannan batu na tallafin Iran ga ‘Yan Houthin.