An Sake Komawa Ruwa A Birnin Aleppo

Birnin Aleppo

Mummunan fada ya sake barkewa a a yau Laraba a Birnin Aleppo dake Syria, yayin da bangarorin biyu da magoya bayansu suka zargi junansu da saba alkawarin tsagaita wuta, a yayin da ake shirya kwashe fararen hula da yan tawayen suka bata lokaci akai.

Kungiyar Saka ido ta Syria don kare hakkin dan Adam, tace tashin hankalin ya hada da harin jiragen sama akan ragowar wuraren da Yan tawayen ke rike da su a Aleppo, Wanda yan tawayen suke rike da su tsahon shekaru 4 da suka wuce. Wuraren yan tawayen sun fuskanci bama bamai, yayin da Gidan Talabijin na Syria yake bada rahoton bama baman da yan tawayen suka jefa ya kashe mutane 6 a yankin da gwamnati ta kwace kwanan nan .

Rasha ta zargi Yan tawayen da karya alkawarin a ranar Talata , inda tace sun farwa jami’an gwamnatin Syria da ke adawa dasu. Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyib Erdogan yace dakarun gwamnatin Syria ne suka fara kai harin . Erdogan da Shugaban Rasha Vladmir Putin zasu tattauna a kan al’amarin na Aleppo a ranar Laraba.

Rasha da ke goyon bayan shugaban kasar Syria Bashar Al-asad da kuma Turkiya dake goyon bayan Yan tawayen da suke son hambarar dashi daga kan mulki, sun cimma yarjajjeniya wanda ya jawo shirin kwashe fararen hular da ake sa ran yi a yau Laraba.