An Sake Gano Wata Mata Dauke Da Cutar Coronavirus a Amurka

coronavirus

A Amurka, an gano wata mata wadda ita ce ta biyu da ta kamu da cutar Coronavirus a yau Juma’a, a cewar jami’an kiwon lafiya.

Matar ‘yar birnin Chicago dake jihar Illinois, ranar 13 ga watan nan na Janairu ta dawo daga birni Wuhan na China, ta na nuna alamomin kamuwa da mummunar cutar mai shafar numfashi, amma sai bayan ‘yan kwanaki ta sanar da likitan ta cewa ba ta da lafiya. Ana kyautata zato a garin Wuhan, babban birnin lardin Hubei, a nan mummunar cutar ta fara.

Rahotannin sun bayyana cewa matar, mai kimanin shekaru 60 da haihuwa na saman sauki amma ta na kwance a asibiti saboda kokarin dakile yaduwar cutar, a cewar Dr. Allison Arwady, shugabar hukumar lafiyar Chicago.

Yanzu haka dai ana sa ido akan mutanen da suka yi huldar kud-da-kud da matar.