An sake dage zabukan wadansu majalisun tarayya

Shugaban hukumar zaben Najeriya Prof. Attahiru Jega

Babban jami’in zabe a Najeriya yace za a sake dage zaben majalisar dokoki ta kasa a wadansu sassan kasar

Babban jami’in zabe a Najeriya yace an sake dage zaben majalisar dokoki ta tarraya a wadansu sassan kasar sabili da rashin isassun katunan zabe. Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Attahiru Jega ya bayyana jiya alhamis cewa, an dage zabe a kimanin kashi goma sha biyar bisa dari na mazubun kasar. Shugaban hukumar zaben yace mazabun da abin ya shafa sun hada da mazabar Bayelsa ta tsakiya, da Binuwe ta arewa da Cross Rivers ta kudu da Cross Rivers ta tsakiya. Sauran kuma sune, Ebonyi ta tsakiya, da Ekiti ta tsakiya da ta arewa da kuma ta kudu. Sai kuma Gombe ta arewa, da Kaduna ta arewa da Niger ta Kudu, ta Plateau ta tsakiya da ta kudu da kuma ta arewa. Bisa ga cewar Farfesa Attahiru Jega, mazabun majalisun wakilai na tarayya da aka dakatar da zaben sun hada da Abekuta ta Arewa, da Akoko Edo, da Gwarzo/Kabo, Da Ifako Ikaiye. Sai kuma Sholu, da Ikorodu, da Katsina Ala/Akum da Isialangwa ta Arewa da ta Kudu. Sai kuma mazabar Jos ta arewa da Bassa da kuma Patakwal 2. Shugaban hukumar zaben yace za a gudanar da zabe ranar Talata ishirin da shida ga watan Afrilu a wadannan mazabun.