An Sakawa Boko Haram Takunkumi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon.

​Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ta amsa kukan Najeriya Alhamis dinnan, na sakawa Boko Haram takunkumi domin yanke hanyoyin samun kudadensu da makamai.
Litinin ne ranar da Najeriya ta nemi a dauki wannan mataki bayan barkewar hare-hare daga ‘yan bindigar. Kwamitin ya hanzarta, inda ya saka sunnan kungiyar a cikin jerin sunayen kungiyoyin dake da takunkumi, wanda kuma ya kwace ikon mallakar ‘yan kungiyar, da hana su sayan makamai.

Jakadan Australiya, Gary Quinlan wanda ke shugabantar kwamitin takunkumi na al-Qaida ya gayawa manema labarai cewa wannan shine matakin farko domin yanke taimakon da Boko Haram take samu daga kasa da kasa.

Takunkumin wani yunkuri ne na hana “mutanen dake sha’awar baiwa kungiyar tallafi” kamar na kudi, ko ta sayar musu da makamai, Quinlan yace, sannan ya kara cewa kwamitin na nufin “dakatar da duk wani taimako da kungiyar take samu.”

Boko Haram mai tunga a arewa maso gabashin Najeriya, ta kashe dubban mutane tun shekatara 2010, a adawar da takeyi da gwamnati.