An Sace Wani Matashi Dan Kasar China A Amurka

Hukumomin Amurka na neman taimakon jama’a wajen gano wani matashi mai shekaru 28 da haihuwa, dan kasar China kuma wanda ya bace tsawon makonni 5 yanzu, mutumin da aka sace a kudancin jihar California, kuma ana kyautata zaton wasu mutane biyu da suka san shi ne suka sace shi.

Hukumar binciken manyan laifukan Amurka da ake kira FBI da kuma wasu hukumomin tsaro na kasar na neman Tony Liao Ruochen, wanda ya bace tun ranar 16 ga watan Yuli, gani na karshe da aka yi masa shine a lokacin da ya fito daga wani taron masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci da aka yi a birnin San Gabriel, gabas da birnin Los Angeles.

Da farko barayin sun bukaci a basu kudin fansa dala miliyan 2 amma kuma ba a kara ji daga garesu ba tun daga lokacin, kuma ba a biya kudin fansar ba.

Hukumomi sun fidda zanen wani mutum ranar litinin da suka bayyana suna shi a matsayin David, wanda suke kyautata zaton yana daya daga cikin barayin kuma ya halarci taron da Liao ya je.

Amma hukumomin basu bayyana sauran mutanen biyu da ake gani su suka sace mutumin ba, suna dai kyautata zaton duka mutanen 3 ‘yan kasar China ne.