An samu tashin hankalin sakamakon danyen hukumcin kisan gilla da aka yi wa wani dalibi dan shekarar karshe ga kammala jami'ar a fannin kimiyar harhada sanadarai Sato Biochemistry.
Daliban na jami'ar kimiya da kere kere ta jihar Kebbi sun nuna rashin yardar su ga abinda ya samu dan uwansu wanda ya yi sanadiyar mutuwar sa.
Dalibin mai suna sharfudeen Sale Kanya ya gamu da ajalinsa ne sanadiyar wata tankiya da ta faru tsakaninsa da wani mai sayar da wayar salula, wanda ke bin dalibin kudi naira 3,500 ragowar kudin wayar da ya saya.
Dalibin yace ya tura masa sauran kudin ta bankin sa kuma an tura masa sakon an cire kudin amma mai wayar ya ce shi baiga kudin ba, abin da yasa ya yi masa ihun barawo
Gwamnatin jihar Kebbi ba ta yi kasa a guiwa ba ganin daliban jami'ar sun dauki niyyar zasu afkawa mutanen gari don daukar fansa.
Rundunar 'yan sanda ta jihar a ta bakin kakakin ta DSP Nafi'u Abubakar ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Yanzu dai mahukunta a jami'ar sun sanar da rufe jami'ar har sai an baiwa daliban tabbacin yin adalci akan abinda ya faru.
A saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Sale Kanya, jihar Kebbi, Nigeria, da Najeriya.