A yanzu haka an rattaba hannu akan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da aka gyara a tsakanin jam’iyyun adawa dake yaki da juna a Sudan ta Kudu don kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru biyar ana yi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane gami da korar miliyoyi daga gidajen su.
Shugaban kasa Salva Kiir, tare da shugaban 'yan adawa Riek Machar, da sauran wakilan jam’iyyun adawa sun rattaba hannu akan yarjejeniya karshe a makwabciyar kasar Ethiopia a jiya laraba.
Duk da cewar gwamnati na murna da wannan yarjejeniya, masu sa ido na kasa da kasa na tababa akan yarjejeniyar. Wata kungiyar raji dake da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka, mai suna Enough Project, ta yi tambaya akan yarejejeniyar musamman akan bayyana rashin ma’anar dubawa da daidaito kan zargin shugaban kasa da amfani da karfin mulki wajen sace dukiyar kasar gami da daukan mummunan mataki na tashin hankali akan 'yan adawa.