An rantsar da Shugaba Bah Ndaw ne a ranar Juma’a a Bamako babban birnin kasar inda zai kwashe wata 18 yana mulki.
A dalilin haka, ake fatan kungiyar ta ECOWAS mai mambobi 15 za ta sanar ko za a dage takunkumin da aka sakawa Malin.
A ranar jajiberin bikin rantsurwar, Ndaw ya gana da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da kungiyar ECOWAS ta nada a matsayin mai shiga tsakani na musamman a rikicin na Mali.
Jonathan ya ce kungiyar ta ECOWAS za ta auna ta ga ko nadin ya yi daidai da bukatun da ta gabatar domin a ga ko za a dage takunkumin da aka saka mata.
Tun dai a ranar Laraba tsohon shugaban na Najeriya, ya fadawa manema labarai cewa, ECOWAS ta gamsu da yadda sojojin suke aiwatar da bukatun kungiyar.
Ndaw shi ne shugaban dakarun kasar ta Mali da suka kwace mulki a hannun shugaba Boubacar Ibrahim Keita.