An rantsar da shugaban kasa mace ta farko a kasar Brazil

Shugabar kasar Brazil Dila Rousseff

An rantsar da shugaban kasa mace ta farko a kasar Brazil.

Wata ‘yar gwaggwarmayar neman ‘yanci da aka gasawa akuba a zamanin mulkin kama karya a kasar Brazil ta zama shugabar kasar mace ta farko. Dubban mutane suka yi tururuwa bisa titunan Brasilia, babban birnin kasar, duk da ruwan saman da aka rika tafkawa kamar da bakin kwarya, suna yiwa Dilma Rousseff shewa yayinda take kan hanyarta zuwa bukin daukan rantsuwa na tarihi jiya asabar a cikin wata mota kirar Rolls Royce, inda wata tawagar jami’an tsaro da ta kunshi mata zalla, ta rufa mata baya. Ms. Rosseff ‘yar shekaru 63 tace shugabancinta ya shata wani sabon babi. Ta kuma ci alwashin karrama mata da kuma kare hakkin marasa galihu, sai dai tace zata tabbatar da ganin an yiwa kowa adalci. Sabuwar shugabar kasar Brazil din , ‘yar wani dan ci rani dan asalin kasar Bulgeriya, ta shiga kungiyar masu ra’ayin rikau dake adawa da mulkin kama karya na soji cikin shekara ta dubu da dari tara da sittin. An daure ta na tsawon shekaru uku, a lokacin kuma tace a gasa mata akuba. Shugaba Rousseff ta gaji kujerar ne daga shugaba Luiz Inacio Lula da Silva, malaminta a fuskar siyasa wanda yayi amfani da gagarumin farin jinni da yake da shi wajen taimaka mata darewa kujerar shugaban kasar.