Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kirista sun halarci sujadar lahadi bayan harin bom da ya yi sanadin mutuwar mutane 21 a Misira


Ma'aikatan kashe gobara a Misira suna kashe wuta bayan harin bomb a majami'ar Coptic dake birnin Alexandria, 01 Jan 2011
Ma'aikatan kashe gobara a Misira suna kashe wuta bayan harin bomb a majami'ar Coptic dake birnin Alexandria, 01 Jan 2011

Kirista sun halarci sujadar lahadi bayan harin bom da ya yi sanadin mutuwar mutane 21 a Misira

Kirista sun halarci sujadar lahadi a majami’ar Coptic ta Misira kwana daya bayan harin kunar bakin waken da aka kaiwa masu aikin ibada a majami’ar da ya yi sanadin mutuwar mutane 21 wadansu da dama kuma suka ji raunuka. Ana iya ganin jini da ya famtsama a ko’ina yayin sujadar. Shaidu sun ce bayan harin da aka kai kiristocin sun yi kokarin kaiwa wani masallaci dake kusa da majami’ar hari, abinda ya haddasa barkewar fada da yayi sanadin raunata wadansu. Shugaban kasar Misira, Hosni Mubarak ya yi Allah wadai da wannan harin, tare da cewa, bai kamata aikin ta’addanci ya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin Kirista da Musulmin kasar ba. Mr. Mubarak ya dora alhakin harin kan wadansu ‘yan kasashen ketare, ya kuma ci alwashin murkushe duk wata makarkashiyar gurguntar da harkokin tsaron kasar. Shugaban Amurka Barack Obama shi ma ya yi Allah wadai da harin. An kai harin ne a kofar majami’ar da kirista suka taru suna addu’oin shiga sabuwar shekara. Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

XS
SM
MD
LG