Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon babban Sufeton 'Yan sandan kasar.
Hakan ya biyo bayan murabus da Ibrahim Idris ya yi ne bayan cika shekaru 60 a duniya.
Ka'idar aikin gwamnati a Najeriya shi ne, babu wani ma'aikacin da ka iya kai wa wadannan shekaru bai yi murabus ba.
Sabon sufeton 'yan sandan dai shi ne Mohammed Adamu Abubakar wanda dan asalin garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa ne.
Kafin nadin na sa, Abubakar malami ne a cibiyar horas da dabarun mulki da muhimman bukatu na kasa wato "National Institute of Policy and Strategic Studies" NIPSS da ke kuru a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Pilato.
Ya kuma taba rike mukamin kwamishinan 'yan sanda a jihohin Ekiti da Enugu kana ya yi mataimakin babban sufeton 'yan sanda mai kula da shiyya ta 5 da ke da hedkwata a birnin Benin.
Tuni dai har sabon babban Sufeton ya fara aiki.
A 'yan kwanakin nan, an yi ta nuna matsin lamba ga gwamnatin shugaba Buhari kan ya sauke Ibrahim Idris daga mukaminsa na Sufeton 'yan sandan Najeriya, domin shekarunsa sun kai munzalin yin ritaya.
'Yan adawa sun yi ta zargin cewa fadar shugaban na kokarin kara wa'adin Idris domin ya jagoranci harkar tsaro a zaben da za a yi a watan Fabrarai, zargin da gwamnati ta musanta.