An Rantsar Da Sabon Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule

Jim kadan bayan rantsar da shi, sabon gwamnan ya yi jawabin irin halin da jihar take ciki, inda ya ce yasan jihar na fuskantar karanci kudi.

Sabon gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayinsa na gwamnan jihar.

Tun da safiyar yau ne aka jibge jami’an tsaro a sassa daban-daban na filin Lafia Square da kewaye don tabbatar da an yi bikin rantsarwa ba tare da wata matsala ba.

Wasu mazauna jihar Nasarawa sun bayyana ra’ayoyinsu kan abin da suke bukatar sabon gwamnan ya fuskanta, inda suka ce suna fama da rashin aikin yi tare da kuma yi masa fatan alheri.

Gwamnan Sule, ya ce al’umar jihar na bukatar hanyoyin inganta tattalin arzikinsu.

Sannan ya kuma kara da cewa ya san jihar tana fama da rashin kudi saboda rashin samun kudaden da ya kamata da suke shigowa jihar.

A bangaren guda kuwa, tsohon gwamnan jihar ta Nasarawa, Umaru Tanko Almakura, ya yaba da goyon baya da al’umar jihar suka ba shi.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Lafia:

Your browser doesn’t support HTML5

An Rantsar Da Sabon Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule