An Rantsar Da Masu Ruwa Da Tsaki A Shari'ar Trump

Majalisar Dattawan Amurka ta bude shari’a kan batun tsige shugaban kasa Donald Trump daga mukaminsa, inda Alkalin Alkalan Amurka ya rantsar da yan Majalisar Dattawa masu shari’a, wanda suka yi alkawarin tabbatar da adalci.

Sa’o’i kafin rantsar da sanatocin, hukumar dake sa ido kan harkokin gwamnatin Amurka mai zaman kanta, ta ce gwamnatin shugaba Trump ta sabawa doka da ta rike kudaden tallafin Ukraine, wani batu da yafi dauke hankali a kan batun tsige shugaban kasar.

‘Yan jam'iyyar Democrat suna zargin Trump da rike kudaden taimakon Kyiv ba bisa ka’ida ba, da zummar tursasa ta ta gudanar da binciken da zai taimaka masa a siyasance a zaben shekarar 2020.

Sai dai Trump, ya musunta aikata ba dai dai ba, yana mai kiran zargin da ake masa da babbar karya a jiya Alhamis. yanzu haka dai Trump shine shugaban Amurka na uku da aka taba tsigewa.

Mallam Hassan Sallau Jibiya, mai fashin baki ne a kan harkokin yau da kullum a Amurka, ya ce Majalisar Dattawan za ta gudanar da shari’ar ne a wata kotu ta musamman da Alkalin Alkalan kasar John Roberts zai shugabance ta.

Ya kara da cewa a ‘yan kwanaki masu zuwa shaidu da dama zasu bayyana a gaban shari’ar, sai dai ya ce babban Alkalin mai shari’ar ne kadai keda hurumin ba da izinin gabatar da masu shaida. A cewar Mallam Hassan Jibiya su ma ‘yan Republican suna iya amfani da rinjaye da suke da shi a Majalisar Dattawan su kare shugaban kasa.

Domin karin bayani saurari hirar Baba Yakubu Makeri da Mallam Hassan Sallau Jibiya:

Your browser doesn’t support HTML5

HIRA DA HASSAN JIBIYA A KAN SIYASAR AMURKA