An Rabawa Dubban Mabukata Kayan Abinci a Iraqi

Hukumar Abinci Ta MDD, ta raba kayan abincin da ake matukar bukatarsu ga 'yan Iraqi sama da 30,000 a birnin Qayyarah da kewaye da ke Arewacin Iraki, mai tazarar kilomita 60 kudu da birnin Mosul.

Garin ya kasance cikin tashin hankali da kuma wuyar shiga na tsawon sama da shekaru biyu.

Rabon kayan abincin da su ka hada da shinkafa da garin alkama da wake da mai na iya rayar da mutanen garin na tsawon wata guda, a cewar hukumar ta abinci a wata takardar bayanin da ta fitar jiya Talata.

An kuma yi wannan rabon ga mutanen da su ka rasa muhallansu su kusan 2,000 da ke zaune a wasu sansanoni da kuma wadanda wasu mutane su ka basu masauki a kewayen Qayyarah.

"Mutanen Qayyarah sun kasance cikin tashin hankali na tsawon shekaru biyu kuma su na fama da matukar yinwa da kuma karancin hanyoyin samun abinci," a cewar Sally Haydock, Shugabar hukumar ta abinci a Iraqi.

A halin da ake ciki kuma, a birnin Bagadaza, wani harin bam da aka kai da mota, ya hallaka mutane 10 tare da raunata 39 a gundumar Karada.

Shugaban Iraqi Fouad Massoun ya yi Allah wadai da wannan harin, to amma ya ce al'amari irin wannan ba zai sa mutanen Iraqi su karaya ba, a kudurinsu na yakar ta'addanci.

Shirin agazawa Iraqi da MDD ke daukar nauyi ya ce munanan tashe-tashn hankula da hare-haren ta'addancin da aka kai a watannin Yuni da Agusta sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 1,450 tare da raunata sama da 2,220 a kasar.