An Nada Thomas Tuchel A Matsayin Kocin Ingila

Thomas Tuchel

Sabon mukamin tsohon kociyan kungiyar Chelsea zai fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.

An bayyana Thomas Tuchel a matsayin sabon mai horas da tawagar kwallon kafar Ingila a yau Laraba, inda kungiyar ta karkata ga bajamushen domin samun damar daukar kofin babbar gasa tun bayan wanda ta daga a 1966.

Sabon mukamin tsohon kociyan kungiyar Chelsea zai fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.

Mai horaswa dan asalin Ingila Anthony Barry, wanda ya taba aiki tare da Tuchel a kungiyar Bayern, zai zamo mataimaki a gare shi.

Tsohon kociyan Ingila Gareth Southgate wanda yayi murabus jim kadan bayan da tawagar tayi rashin nasara a hannun Sifaniya a gasar zakarun nahiyar Turai ta 2024 a watan Yulin daya gabata, bayan rike mukamin tsawon shekaru 8.

Tuchel mai shekaru 51 da haihuwa, wanda ya jima baya aiki tun bayan da bar Bayern Munich a karshen kakar data gabata, zai gaji Gareth Southgate a matsayin mai horaswa na dindindin kuma ya zama mutum na 3 wanda ba dan Ingila ba da zai jagoranci kungiyar ta “Three Lions” bayan Sven-Goran Eriksson da Fabio Capello.

Tuchel, wanda ya taba jagorantar kungiyoyin Borussia Dortmund da Paris Saint-Germain, yana da tarihin daukar kofin da kungiyar kwallon kafar ke bukata domin kawo karshen shekaru 58 data shafe bata lashe wata muhimmiyar gasa ba tun bayan cin kofin duniya da tayi a 1966.