An Nada Shugabannin Hukumar Kula Da Gajiyayyu Ta Najeriya

  • Murtala Sanyinna

shugaba buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nada shugabannin sabuwar hukumar kula da masu larura ta musamman ta kasar.

An kafa sabuwar hukumar ta kula da masu nakasa da ke bukatar kulawa ta musamman ne bisa tanadin dokar yaki da kyamar masu nakasa ta shekara 2019.

Tsohon dan majalisar wakilai daga Jihar Kebbi Husseini Suleiman Kangiwa shi ne sabon shugaban hukumar, a yayin da aka nada Abba Ibrahim daga Arewa Maso Gabas a matsayin Sakatare.

Wannan hukumar na da manufar kula da masu larura ta musamman da yawan su ya kai miliyan 25 a Najeriya, ta hanyar samar da karin kashi 5 cikin dari na aiyukan yi, da kuma ba su kulawa ta musamman akan batutuwan da suka dame su a dukan fanoni na rayuwa da kiwon lafiya da kuma harkokin walwalarsu da nufin share masu hawaye.

Daya daga cikin shugabanin kungiyoyin masu larurar na kasa sakamakoni cutar shan inna Misbahu Lawal Didi ya ce yanzu ne masu fama da nakasa za su fara samun damar shiga a dama da su a harkokin mulki a Najeriya.

Misbahu ya yaba da wanan kokari da Gwamnati ta yi, wanda ya ce dama sun dade suna jiran irinsa, domin baiwa mutanensu damar ba da ta su gudummuwa a harkokin cigaban kasa, wanda hukumar za ta taimaka masu gaya wajen cimma wannan burin.

Abin da ya dauki hankali a yanzu shi ne kulawar da mata masu nakasa za su samu, la'akari da irin rawar da suka taka a lokacin gwagwarmayar kafa wanan hukuma.

Shugabar mata masu larura a kasar, Rabi Yusuf Gezawa, ta ce za su ci gaba da fafutukar tabbatar da ba a bar mata a baya ba a wajen cin gajiyar hukumar.

Rabi Gezawa ta ce sun fito kwansu da kwarkwata a kokarin ganin an samu Hukumar ta kula da masu bukata ta musamman duk da cewa suna da aure inda ta yi rokon kar maza su danne su a yanzu da kwaliya ta biya kudin sabulu.

Mashawarci na musamman ga shugaban kasa a lamurran masu larura ta musamman Shehu Garba, ya shawarci 'yanuwansa da su sakawa wannan kokari na Gwamnati ta hanyar yin addu'o'i da fatan alheri.

Ya ce wannan dama ce da gwamnatin ta sama musu na more romon damokradiya tunda ta nuna masu kauna tareda ba su kafa na samun hakkokin su a cikin sauki ta hanyar hukuma da za ta kula da lamuran su.

Ga cikakken rahoton Madina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

An nada shugabannin sabuwar hukumar kula da gajiyayyu ta Najeriya