Burtaniya ta nada Ministar Kadaici don kula da masu fama da kadaici, wadanda aka ce yawansu ya kai misalin kowane mutum 1 daga cikin ‘yan Burtaniya 10.
Ministar Wasanni Tracey Crouch za ta kara wannan mukamin kan wanda take rike da shi na yanzu don ci gaba da aikin da tsohuwar ‘yar majalisar dokoki marigayiya Jo Cox da aka kashe, ta fara bayanda ta kafa kwamitin kula da kadaici a 2016.
“Ga mutane da yawa, kadaici wani bangare ne na rayuwar yau da kullum ta wannan zamani,” a cewar Firaminista Thersa May a jiya laraba, inda taci gaba da cewa, “Ina son in fuskanci wannan matsalar ga al’ummarmu kuma ina fata kowa zai dau mataki don magance kadaicin da tsoffi da sauran marasa karfi da wadanda suka rasa danginsu kan yi fama da shi -- ma’ana mutanen da ba su da wadnda za su yi magana da su.”
Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta Burtaniya ta ce ‘yan kasar wajen miliyan tara kan bayyana kansu a matsayin masu fama da kadaici daga cikin jimalar mutane miliyan 65.6.
Mutanen sun hada da wadanda wani lokaci sukan share fiye da wata daya basu yi magana da ko mutum guda ba.