Nadin sabon sarkin na kushe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sanya hannun sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim.
Idan za a tuna dai, a ranar Lahadi da ta gabata ne Sarkin Ningi, Alhaji (Dr.) Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu yana da shekara 88 a duniya bayan ya mulki masarautar na tsawon shekaru 46.
A cewar wasikar, an dauki wannan matakin ne bisa dogara da karfin iko da aka bai wa gwamnan kan doka Cap. 24 Item 3 (1) na dokokin jihar Bauchi kan nadin sarakuna ta shekarar 1991 kuma bayan shawarar da masu alhakin zabin sabon sarkin suka bayar.
Da safiyar Jiya Lahadi, 1 ga watan Satumban shekarar 2024 masarautar kasar Ningi, ta gudanar da nadin sabon Sarkin a masarautar Kasar Ningi, bayan shafe shekaru 47 da marigayin ya yi a kan karagar mulki.
An gudanar da bukukuwan nadin ne a Fadar Sarkin, inda aka samu halartan masu rike da Sarautun gargajiya na masarautar da kuma kusoshin gwamnatin jihar Bauchin.
Mohammed Sabo Abubakar magatakardan Ningi, ya bada takaitaccen tarihin sabon sarkin inda ya ce an haifi Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya a shekarar 1956 kana ya yi karatu a Maiduguri a lokacin mahaifinsa tsohon sarkin yake aiki a Hukumar Harkokin Kasuwanci ta Najeriya a Maiduguri. Ya kuma yi karatu a Kwalejin Aikin Noma A Bauchi.
Sabon Sarki Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya, ya fara a aiki a Hadeja Jam’are River Basin Development Authority. A lokacin da mahaifinsa ya zama sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya ya dawo fada ya taimaka wa mahaifinsa a matsayin magatakardansa. Kana daga bisani aka yi masa sarautar Ciroman Ningi, haka zalika aka tabbatar da shi hakimin Ningi.
Akwai Gidajen Zuriyar Sarauta a Ning da suka hada da zuriyar Gidan Malam Hamza, Akwai zuriyar gidan Malam Abubakar Dan maje da kuma zuriyar gidan Malam Usman Danyaya
Ga sautin rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi:
Your browser doesn’t support HTML5