Gamaiyar kungiyoyin arewa ta CNG a takaice ta sha alwashin maida hankali kacokan kan shawarar hanyoyin magance kalubalen tsaro da ke addabar yankunan arewacin Najeriya.
kungiyar ta ce nazarin da ta yi, ya nuna a zahiri yankin na arewa bai samu tsaron rayuka da dukiya ba. Lamarin da ya sa da wuya yankin ya sake farfadowa kamar yanda ya ke a shekarun 1980 ba.
A taron manema labarai domin gabatar da wasikar nada jigon gamaiyar kungiyar Abdul'aziz Sulaiman, a matsayin kakakin majalisar dattawan arewa domin ya maye gurbin Dokta Hakeen Baba Ahmed da ya karbi mukami a gwamnatin Ahmed Tinubu, shugaban gamaiyar Jamilu Aliyu Charanci yace sai kowa ya ba da gudunmawar sa bisa tsari sannan ne za’a kai ga cin nasara.
Jamilu Charanci ya ce hatta daukar 'yan sa kai ya na bukatar kwarewa wajen bincike domin yi wa kowa adalci, wanda shi ne jigon samun nasara.
A jawabin shi sabon jami'in yada labarai na kungiyar dattawan ta arewa da farfesa Ango Abdullahi ke jagoran ta Malam Abdul'aziz Sulaiman, ya ce ya zama wajibi 'yan arewa su hada kai wajen kawar da bambance-bambance da fuskantar abubuwan da za su dawo da zaman tare a yankin.
Ita dai gamaiyar kungiyoyin arewa ta kunshi matasa da dalibai, da dattawa 'yan arewa masu shekaru, kuma asali marigayi Danmasanin Kano, Alhaji Maitama Sule ne ya kafa ta, inda sauran dattawa irin su Sani Zangon Daura, Paul Unongo su ka rika taimakawa domin kare muradun yankin, Yankin arewa shine yanki mafi fadi da yawan jama'a a Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5