Karo na biyu Kenan da a ake dawo da yan Najeriya daga kasar Libya, domin ko a ranar 15 ga watan jiya saida wani jirgi ya mayar da wasu yan Najeriya 150 daga Libya.
Alhaji Idris Abubakar Muhammed dake zama babban Jami’in hukumar ta NEMA, wanda ke kula da shiyar Legas yayi karin haske game da yan Najeriyan da aka mayar da su gida. Inda ya ce sun karbi ‘yan Najeriyan ne karkashin wani shiri na gwamnatin tarayyar Najeriya.
Aksarin yan Najeriyar da ake dawowa da su dai suna zuwa kasar ta Libya ne da zummar ketarawa zuwa Turai domin samun ingantacciyar rayuwa, abin da kesa wasu rasa rayukansu tun a cikin hamadar sahara, wasu kuma su fada hannun masu fataucinn mutane da cinikin bayi.
Yawancin lokuta dai hukumomi na bada shawarwari da kuma daukan matakai na hana kwararan yan gudun hijiran zuwa Turai, amma alamu sun nuna cewar basa jin kira.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5