An Maka Majalisar Dokokin Najeriya A Kotu Kan Sayen Motocin Alfarma

Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa da kuma kare hakkin dan Adam irin su SERAP da EiE da kuma wasu ‘yan kishin kasa su 6,721 sun amince a shigar da kara kan yadda ‘yan majalisar dokoki a Najeriya za su kashe kudi har Naira biliyan 5 da rabi wajen sayen motocin kawa.

Kungiyoyin sun ce sun shigar da kara ne akan suna so a haramta wa majalisar kashe wadannan kudade, saboda ya saba wa kashi na 57 karamin kashi na 4 na tsarin sayayyar kayan amfani na shugabanin majalisar dokokin kasa da aka kirkira a kundin tsarin mulkin majalisar a shekara 2007.

Kungiyoyin sun ce ya zama wajibi majalisar ta zabge yawan adadin kudaden da suke so su sai motocin da su.

Daya cikin 'ya'yan kungiyoyin, Salihu Dantata Mahmood, ya ce ba zai yi wu suna ganin talauci da yunwa da rashin biyan kudaden makarantan yara da rashin magunguna yana daidaita mutane sannan su yi shiru ba, domin ai an zabe su ne domin su yi dokokin da za su canja rayuwar al'umma ba kashe kudade barkatai ba.

Shi ma Komred Bako Abdul, wanda ya wakilci kungiyar Campaign for Democracy a lokacin shigar da karar ya ce almubazaranci ne barin ‘yan majalisar su sayi motoci na yawan wadannan kudade.

Ya kara da cewa, ‘yan majalisar su yi maza-maza su janye wannan kuduri na sayen motoci domin su wakilan mutane ne ba wakilan kansu ba ne.

To wai menene doka ta tanada ne a game da irin wannan mataki na kashe makudan kudade duk shekaru hudu? Barista Mainasara Ibrahim Umar, ya yi karin haske inda yake cewa babu wata doka da ta tanadi kashe irin wadannan kudade, hasali ma su ‘yan majalisar ne su ka yi dokoki iri daban- daban domin kare dukiyar al'umma, amma kuma su ne suke kokarin karya dokokin.

Kokarin jin ta bakin 'yan majalisar ya cutura domin kowanne aka tunkare shi da batun sai ya ki yin magana.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

An Maka Majalisar Dokokin Najeriya A Kotu Kan Sayen Motocin Alfarma