An Kwashe Yini Na Biyu Cikin Dokar Hana Fita a Kaduna

KADUNA: Rikicin Kafanchan

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa duk da kasancewar dokar, an kai hare-hare a unguwannin Narayi da Kaduna ta Kudu, inda aka zargi wasu mutane sanye da kayan soji da aikata kisa.

Yayin da aka shiga yini na biyu bayan da hukumomin jihar Kaduna suka saka dokar hana yawo a ciki da kewayen jihar sanadiyar rikicin da ya tashi, tituna sun kasance fayau yayin da shaguna, makarantu, da kasuwanni su ma suka kasance a rufe.

“Garin na Kaduna ya tashi fayau, babu wani alamun tashin hankali.” Inji wakilin Muryar Amurka Nasiru Yakubu Birnin Yaro.

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa duk da kasancewar dokar, an kai hare-hare a unguwannin Narayi da Kaduna ta Kudu, inda aka zargi wasu mutane sanye da kayan soji da aikata kisa.

Jiradar ta ce mutum uku sun rasa rayukansu a wannan hari na sojoji da ake ganin na bogi ne.

A ranar Lahadi gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasiru El Rufa’i ya saka dokar hana zirga-zirga a jihar, bayan wata tarzoma mai nasaba da addini da kabilanci da ta barke a yankin Kasuwar Magani.

Jami’ai a jihar sun ce akalla mutum 55 suka rasa rayukansu, yayin da jami’an tsaro ke cewa sun cafke mutum 22 da ake zargi da ta da husumar.