An Shirya Kwashe Dubban 'Yan Syria Da Iyalansu Dake Yankin Gabashin Ghouta

An shirya cewa dubban mutanen kasar Syria dake zaune a yankin nan da ake ta rikici a cinkinsa na Ghouta zasu fice tareda iyalansu.

A yau Alhamis ne, aka shirya cewa dubban mutanen kasar Syria dake zaune a yankin nan da ake ta rikici a cinkinsa na Ghouta zasu fice tare da iyalansu a karkashin wata yarjejeniyar da aka kulla a karkashin jagorancin kawar Syria, watau kasar Rasha.

Dangane da hakan ne aka shirya jerin manyan motocin safa-safa da aka ce zasu kwashe mutanen daga Harasta zuwa garin Idlib dake arewancin Syria din, wanda kuma yake karkashin rikon ‘yan adawa.

Wannan shirin yayi kama da wanda aka saba gani a wasu garuruwan Syria a can baya, inda ake samun lokutan da gwamnati ke matsawa mayakan ‘yan tawaye lambar su kwashe mutanensu, su koma yankunan dake hannun ‘yan tawayen.

Hari ila yau, wannan yarjejeniyar ta yau ta kunshi musayar fursunonin yaki tsakanin gwamnatin Syria da mayakan ‘yan tawayen.

Tun a cikin watan jiya ne dai gwamnatin Syria, tareda goyon bayan Rasha, ta kaddamarda munanan hare-haren jiragen saman yaki akan yankin gabashin Ghouta, abinda ya janyo halakar mutane 1,500.