Matakin na RTUK na kwace lasisin tashar Acik Radio mai mazauni a Istanbul, wadda ta fara yada shirye shiryen ta a shekarar 1995, ya biyo bayan wani bako da aka gayyato a ranar 24 ga watan Apirilu, wanda yayi wata baram barama akan kisan kiyashin Armenia.
Bakon da aka yi hira da shi a tashar yayi baram baramar ne inda yace, a bana an haramta bikin tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar Armeniya
Ranar 24 ga Afirilu ta kasance wata rana ta tuna yakin duniya na daya, lokacin da daular Ottoman, wanda ya gadar da Turkiyyar wannan zamanin ta kashe dubbun dubatan Armeniyawa. A shekarar 2021 ne, a karon farko, Shugaban Amurka Joe Biden, ya amince da ranar 24 ga watan Afirilu, a matsayin ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa Armaniyawa.