A filin wasa na Teslim Balogun dake birnin Ikko a Najeriya, aka kirga kuri’un zaben fidda gwani na dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC mai adawa.
An kirga kuri’un kowani dan takara ne a lokaci daya, kafin a kammala tantance jimlar kuri’un da kowani dan takara ya samu.
‘Yan takarar sune tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso, gwamnan Imo Rochas Okorocha, tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da shugaban kamfanin jaridar Leadership Sam Nda Isaah.
Ga yadda sakamakon yake a halin yanzu, daga wakilin Muryar Amurka, Hassan Umaru Tambuwal.
Atiku Abubakar - 954
Muhammadu Buhari - 3430
Rabi'u Musa Kwankwaso - 974
Rochas Okorocha - 624
Sam Nda Isaah - 10
Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta kammala zaben fidda gwaninta, inda shugaba mai mulki Goodluck Jonathan ya karbi akalar takarar, tare da mataimakinshi Namadi Sambo.
Jaddawalin Sakamakon Zaben Fidda Gwani na Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a APC, daga wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal.
Dan Takara |
Adadin Kuri’u |
Atiku Abubakar |
954 |
Muhammadu Buhari |
3430 |
Rabiu Musa Kwankwaso |
974 |
Rochas Okorocha |
624 |
Sam Nda Isaah |
10 |