Obinna Odo, shine babban injiniyan dake kula da aikin. Ya kuma shaida wa Muryar Amurka cewa aikin wanda gwamnatin tarayya ke gudanarwa a karkashin hukumar raya yankin Niger Delta (wato NDDC) na tsawon kilomita 30 ne.
Mr. Odo ya kuma ce, sun fara aikin a makon farko na watan Mayu, kuma suna gab da kammala shi, saboda sun kai kashi 80 cikin 100 na aikin. Ya kara da cewa ruwan sama da ake yi yanzu shi ke kawo jinkiri a aikin. Kuma suna sa ran kammala komai nan da wata daya.”
Wasu sun bayyana farin cikinsu da wannan hanyar da gwamnatin tarayya ta sabunta.
"a hakikanin gaskiya, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi rawar gani wajen bunkasa hada-hadar kasuwanci a garinmu. Yanzu komai na tafiya daidai. An manta da wannan hanyar kimanin shekaru 30 da suka wuce, kuma tunda an gyara ta yanzu, mun godewa gwamnatin tarayya,” inji Mr. Chidi Okeke, shugaban al’ummar Ndi-Aniche-Obinetiti, daya daga cikin garuruwan da hanyar ta bi ta cikinsu.
Yayin da Malama Beatrice Amaka Obioha, ‘yar asalin garin Ndimeokoro-Arondizuogu ta bayyana cewa, “tayi matukar farin ciki saboda an dade ba a kula da wannan hanyar. Ta ce, sai muka zamo tamkar wadanda aka manta da su. An fara aikin kamar wasa, amma sai gashi da gaske akeyi, kuma ana aikin wurjanjan.”
Wasu dai sun shaida Muryar Amurka cewa tun da aka fara gyara hanyar, an samu ragi a kudin mota daga Okigwe zuwa Nnewi, da kuma daga Okigwe zuwa Anacha, wadanda a da can cikin wasu kauyuka direbobi ke bi kamin su isa, yayin da kuma ake sa-ran fara jigilar fasanjoji daga Okigwe zuwa Awka, babban birnin jihar Anambara, wanda har yanzu babu ita.