Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Fallasa Malaman Jami'a Masu Lalata Da Dalibai


Dr Sani Yakubu Gombe
Dr Sani Yakubu Gombe

Hukumar jami'oin Najeriya watau NUC ta bukaci jami'oi da su rika tona asirin malamai masu yin lalata da dalibai don basu maki a jaraba don tozarta su a idon duniya

Shugaban hukumar Farfesa Abubakar Rasheed, ya nemi wannan bukata ganin yadda wannan matsala ta ke kara yawa a tsakanin malamai marar sa mutunci.

NUC ta nemi a duk wata a rika fallasa sunayen irin wadannan malaman don yayata sunayen su a duniya da zaiyana su a matsayin fasikai.

An sha kama malaman jami’o’in Najeriya na lalata da dalibai mata don ba su maki a jarrabawa da hakan kan kawo matukar koma baya a ci gaban ilimi.

Kalubalen ya shafi hatta malamai masu luwadi da dalibai maza don samun maki a jarrabawa.

A zantawa da aka yi da wani malamin kolejin ilimi da fasaha Dr.Sani Yakubu Gombe ya ce wasu daliban baya ga maki, da amincewa miyagun malaman su kan samu kudin biyan karatun su ko daukar nauyin karatun.

Dr.Gombe ya bukaci a yi horo mai tsananin gaske ga irin wadannan malaman don hakan ne kawai zai rage mummunar dabi’ar.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:44 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG