An Kusa Fara Gagarumin Shirin Gwaje-Gwajen Cutar Coronavirus a Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a yau Juma’a cewa, nan ba da jimawa ba za’a fara gwaje-gwajen cutar coronavirus mai yawan gaske. Ya kara da cewa tuni aka rage duk wani dogon turancin tsarin gwamnati, to amma kuma bai bada cikakken bayani akan yaushe, ko yaya za a soma gwajin ba.

A shafinsa na twitter, Trump ya ce hukumar yaki da barkewar cututtuka ta CDC ta duba, tare da nazarin tsarin ta na yin gwajin, to amma kuma ba ta yi komai akai ba”, inda ya ci gaba da cewa “shugaba Obama ya kawo sauyin da ya kara rincabe al’amura.

Trump dai bai bada wata shaida ba akan canje-canjen da ya ce tsohon shugaban ya kawo da suka dagula al'amura.

Da safiyar yau Juma’a kuma China ta bayyana wasu sabbin mutane su 8 da suka kamu da cutar coronavirus (COVID-19).

Kafafen yada labaran China sun ruwaito cewa shugaban kasa Shi Jinping, ya shaida wa babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ta wayar tarho a jiya Alhamis, cewa China za ta ci gaba da kokarin shawo kan cutar da hana yaduwarta.