Majalisar tace zai koma matsayin yadda yawan masu sarautun suke a dokar da aka kafa a shekarar 2011, inda ake da masu gundumomi guda 133, sai kuma hakimai guda 657, a maimakon masu gunduma guda 193 dakuma hakimai guda 983 a fadin jihar a dokar shekarar 2015.
Bincike dai ya nuna cewa jam’iyyar PDP ta gudanar da wadannan nade naden ne anas aura kwanaki uku ta mika mulki ga jam’iyyar APC wadda ta lashe zabe. Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi Kawuwa Shehu Damina, yace Majalisa ta karbi rahotan Kwamiti saboda haka za a tsarkake tsarin masarautun.
A cewar ‘yar Majalisa mai wakiltar mazabar Dass, Maryam Bagel, tace bata da ra’ayin rushe masu sarautun, inda tace dalilinta kuwa shine dole a mutunta masarautun gargajiya kar a hada ta da siyasa, domin idan har aka nada sarakuna kuma aka rusa su a duk lokacin da aka ga dama, hakan tamkar an mayar da masarautu kamar na siyasa.
Saurari cikakken rahotan Abdulwahab Mohammad daga Bauchi.
Your browser doesn’t support HTML5