An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Kasar Tasakiyar Afrika ta shafe shekaru da dama cikin rikici tsakanin kiristoci da musulmai, yanzu an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar hadin kan Afrika sun ce, tattaunawa a Khartoum ta kai ga kulla yarjajjeniyar zaman lafiya tsakanin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da kungiyoyi 14 masu dauke da makamai.

Wannan wani abin farin ciki ne da ake kuma fatan alama ce cewa zaman tafiya na tafe bayan tashin hankali na shekaru da dama da kasar ta fuskanta.

Wannan wata rana ce mai matukar muhimmanci ga Jamhuriyar Tsakiyar Afrikan da kuma mutananta gaba daya, a cewar Smail Chergui, kwamishina a kungiyar hadin kan Afrika akan zaman lafiya da tsaro.

Sai dai ba a bayyana sharuddan yarjajeniyar zaman lafiyar nan da nan ba.

Mai Magana da yawun FPRC, daya daga cikin kungiyoyin, Abakar Sabom, ya ce, "mun yadda kan abin da yake da muhimmanci ga kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, wato zaman lafiya.”

Sai dai an taba makamanciyar wannan yarjejeniyar a shekarun baya amma ta wargaje.