‘Yan majalisar dokokin tarayyar Amurka na duka bangarorin siyasar biyu, sun cimma wata yarjejeniya a bisa manufa, ta samar da kudin tafi da gwamnati, da kuma kauce ma sake rufe ma’aikatun gwamnati a karshen wannan makon.
Amma babu ko daya daga cikin wadanda su ka cimma yarjejeniyar da ya bayar da cikakken bayanin abin da ta kunsa, da kuma bayanin ko shin Shugaban Amurka Donald Trump zai iya samun dukkannin kudaden da ya ke bukata don gina katanga a kan iyakar Amurka da ke kudu.
‘Yan Demokarat sun yi tayin samar da wani dan kudi na inganta tsaron kan iyaka - wanda ko kusa bai kai adadin kudin da Trump ya ce ya na bukata don gina katangar ba.
Fadar Shugaban Amurka ta White House da ‘yan majalisar dokokin na fuskantar cikar wa’adin ranar Jumma’a, lokacin da kudin tafi da gwamnati zai sake karewa ga rubu’in ma’aikatun gwamnati.
Don haka suke fadi-tashin kauce ma sake rufe ma’aikatun, makonni uku bayan da aka kawo karshen rufe ma’aikatun gwamnati na lokaci mafi tsawo wato kwanaki 35.