An Kubutar Da Wani Fasto Daga Hanun Boko Haram

Wata gidauniya mai zaman kanta da ake kira Kaltum Foundation da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kan su guda biyu sun kubutar da wasu mutane biyu a hannun Boko Haram sun kuma mika su ga gwamnatin jihar Borno.

Wadannan mutane sun hada ne da limamin wata cocin Living Faith Church dake a Maiduguri, Fasto Moses Oyeleke da wani dan'uwansa da aka yi garkuwa da su watanni bakwai da suka gabata, yayin da suke hanyar su zuwa garin Chibok, a dai dai lokacin da suka isa garin Bama kafin su shiga Chibok.

Fasto Moses Oyeleke da aka kubutar da shi a ranar Lahadi, yace har yanzu dan uwansa na nan a hannun mutanen da suka yi garkuwa da su. Fasto Moses yace ya yi matukar farin ciki da ya dawo gida. Sai dai ya kara da cewa babu wata azaba da aka gana masa yayin da yake hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Da yake zantawa da wakilin Muryar Amurka a Maiduguri, Fasto Moses Oyeleke yace masu garkuwa da shi sun nemi ya musulunta ya bar addininsa amma kuma ba tare da wata tsangwama ba, ya kuma ce sun yi zaman lafiya da shi a tsawon lokaci da ya kwashe a wurinsu.

Wata yarinya ‘yar shekaru 14 da kungiyoyi masu zaman kansu suka kubutar da ita bayan an sace ta a gidansu dake wani kauye a cikin karamar hukumar Askira Wuba dake kudancin jihar Borno, mai suna Jagilaye Ibrahim, ta bayyanawa Muryar Amurka irin hali da fada a ciki a hannun ‘yan Boko Haram.

Jagilaye Ibrahim, tace ta kwashe watanni tara a hannun masu garkuwa da ita ta kuma ga ana tursasa wa wasu ‘yan mata da suma ake garkuwa da su ana aurar da su, sai dai tace ba a yi mata irin wannan auren ba.

Daga Maiduguri, ga rahoton Haruna Dauda a kan wannan batu:

Your browser doesn’t support HTML5

AN CETO MUTANE BIYU DAGA BOKO HARAM