Kimanin watanni uku kenan gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokin shiga kasar ta tsandauri, lamarin da ya dakile harkokin kasuwanci ta wadannan wurare, harma ‘yan kasuwa ke ci gaba da kokawa.
Koda yake hukumomin na Najeriya ba su bayyana dalilan su ba gabanin daukar wannan mataki, amma daga bisani sun yiwa ‘yan kasa bayani game da hujjar yin hakan.
Alhaji Bello Isa Bayero daya daga cikin dattawan arewa kuma makusanci ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara jaddada wadancan matakai da gwamnati ta dauka, inda ya ce mutane basu da hakuri akan irin matakan da gwamnati ta ke dauka wajan magance fasakobri.
Matakin rufe iyakar dai ya katse ko ya raunana hanyoyi da harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin Najeriya da wasu kasashe makwabtan musamman ta bangaren arewacin kasar.
A hannu guda kuma, a hira da wakilin sashin Hausa na Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari, ya yi da tsohon ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce koda yake matakin rufe iyakokin shiga kasar ta tsandauri, ka iya zama mai alfanu, amma gazawar gwamnati wajen daukar matakan da suka dace da kuma rashin ilimantar da 'yan kasa kafin rufewar na daga cikin kalubalen da zasu hana yunkurin cimma nasarar da ake bukata.
Saurari cikakken rahoton wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:
Facebook Forum