Dan Majalisar Dokoki ta jihar Sakkwato mai wakiltar mazabar Gada ta gabas Honorabul Haruna Dauda ya ce an ceto yaran ne bisa ga kokarin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da hadin guiwar gwamnatin jihar Sokoto.
SAKKWATO, NAJERIYA - Yace Kwamandan garison na sojojin Najeriya dake Sokoto ne ya hannunta yaran da wasu mata da aka ceto su goma sha takwas.
A cewarsa, Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu, ya umurci a duba lafiyar mutanen da aka ceto kuma dukkansu na cikin koshin lafiya.
Gwamnatin Sokoto daga bisani ta hannunta mutanen ga Shugaban karamar hukumar Gada da sauran shugabannin yankin domin a sadar da su da iyalansu.
Ku Duba Wannan Ma SOKOTO: 'Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Makarantar Allo Da DamaRanar Jumu’a, 8 ga watan Maris ne ‘yan bindigar suka kai samame suka sace almajiran da wasu mata a kauyen Gidan Bakuso a karamar hukumar Gada dake gabasin Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.