Hukumomi a kasar Kamaru sun kona ton 60 na magungunan jabu da aka kama a kasar a cikin wannan makon.
Wani jami’in kwastam na Kamaru, Marcel Kamgaing, ya ce wadannan magungunan sun hada da na warkar da ciwon sukari, da hawan jini, da sankara ko daji, kuma an shigar da su ne domin sayar wa ga jama’a a kantunan magunguna da kuma gefen hanya.
Ya kara da cewa wadannan magunguna na jabu suna da matukar hatsari ga lafiyar jama’a, kuma suna iya kashe masu amfani da su.
An shirya kona magungunan a daidai lokacin da kasashen duniya ke shirin hallara a kasar ta Kamaru domin yin taro a kan matsalar magungunan jabu a nahiyar Afirka.
Shugaban kungiyar lauyoyi a kasar Kamaru, Jackson kamga, ya ce irin hukuncin da dokokin kasar suka tanada a kan masu sayar da magungunan jabu, baya da tsananin da zai iya zamowa hannunka-mai-sanda ga duk masu shirin shiga wannan mummunan safarar.