An Kira Gwamnatin Najeriya Ta Yiwa Harkokin Jiragen Sama Garambawul

Matattun jiragen sama a Legas, Najeriya

Kungiyar masu kula da zirga-zirgan jiragen sama a Najeriya ta kira gwamnatin tarayya ta yiwa harkokin jiragen sama garambawul domin tabbatar da tsaron lafiyar matafiya

A babban taronta na shekara shekara da tayi a Jos fadar gwamnatin Filato kungiyar ta bayyana takaicinta kan halin da harkar jirgin sama ya fada .

Matsalolin kuwa sun hada da rashin kyawon hanyoyi da jiragen sama ke sauka da inganta wasu naurorin da ake kula da jiragen musamman yayinda suke shawagi a sararin samaniya.

Shugaban kungiyar yace manufar taron shi ne su tattauna hanyoyin inganta harkokin jiragen sama domin habaka tattalin arzikin kasar.

Shugaban yace kungiyar ta yaba da hankoron gwamnati na kawar da cin hanci da rashawa wanda acewarsu zai bada fifiko da yin gyara a bangarorin da suka shafi rayuwar al'umma. Yace ba sai an samu hadarin jirgin sama ba za'a soma guje-gujen yin gyara. Yace harkar jirgin sama lamari ne na bai daya a duk fadin duniya.

Acewar shugaban Najeriya tana bayan kasashen duniya a yadda ake kula da harkokin jiragen sama.

Shi ma sakataren kungiyar yace basu da isassu da ingantattun kayan aiki kamar naurorin dake taimakawa a san halin da jirgi ke ciki yayinda yake balaguro a sararin samaniya.

Alhaji Bello Abdulmummuni yayi karin bayani akan yadda gwamnati zata inganta harkokin jiragen sama a kasar. Ya kira a horas da ma'aikata a kara kayan aiki na zamani.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kira Gwamnatin Najeriya Ta Yiwa Harkokin Jiragen Sama Garambawul - 3' 42"