An kira a hade jihohin Najeriya 36 zuwa shiyoyi shida

Tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo

Tsohon sakataren kungiyar kasashen renen Ingila Chief Emeka Anyaoku ya kira ga majalisun tarayyar Najeriya su bullo da dokokin da zasu hade jihohin kasar 36 zuwa shiyoyi shida

Chief Anyaoku yace su bar jihohin a matsayin yankunan raya kasa saboda taimakawa cigaba.

Yayi wannan kirar ce a lokacin da yake gabatar da wata kasida a jam'ar Ibadan jiya Litinin.

Yace yau jihohin talatin da shida basu da wani sukuni har ya kai basu iya biyan albashin ma'aikatansu kana da yawansu suna ta wadari ne cikin basussuka. Yace lokacin da kasar ke da larduna hudu ta cigaba da albarkatun da take dashi. A lokacin ana samun gyada daga arewacin kasar, koko daga yammaci roba daga tsakiyar kasar da manja daga gabashi. Amma yanzu babu cigaba.

A jawabinsa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo cewa ya yi dole ne majalisun tarayyar Najeriya su daina yin anfani da al'adan nan ta kariya su kasawa 'yan Najeriya komi a fili kana su guji cin hanci da rashawa.

Obasanjo ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta yaki zaman kashe wando da ya yiwa kasar katutu. Yace ta maida hankali wajen samarda tsaro musamman a arewa maso gabashin Najeriya inda ake yin tashin tashina..

Babban bako mai jawabi maanin tarihin kasa da kasa da siyasa daga kasar Amurka Richard Yusuf yace akwai ababen tambaya game da Najeriya.

Ga karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

An kira hada jihohin Najeriya 36 zuwa shiyoyi shida - 2' 53"