An Kera Motar Farko Mai Hade Da Wayar Zamani

Police tech

Shekara guda kenan da kamfanin Google yayi kokarin kirkiro yadda za’a kera motoci hade da fasahar wayoyin hannu irin na zamani, domin kokarin kawo karshen ‘dauke hankalin direbobi wajen tuki da amfani da waya alokaci ‘daya.

Kirar mota Hyundai Sonata 2015 itace motar farko da ke ‘dauke da wannan fasaha wadda ta hada da mujallar aika sakon rubutu ko murya, da yin kira da amsa waya, sauraren wake-wake da ma sauran muhimman fasahahohin da wayar hannu ke dauke dasu, za kuma a iya sarrafa su ta hanyar danna yatsa kan allon dake gaban mota.

Hyundai yace suna aiki domin kawo sauran fasalolin dake hade cikin manhayar Android kafin karshen shekarar nan. Kamfanin dai ya hada gwiwa da kamfanonin kera motoci har guda 30 domin ganin an samu amfani da fasahar a sababbin motoci masu zuwa, kafin wannan lokaci idan mutum ba zai iya hakura har sai sauran motoci sun fara hada wannan fasahar a motocin da suke kerawa, to sai nemi motar Hyundai Sonata 2015 daga yau domin amfanar sabuwar fasahar.